Dan wasan kasar Faransa da ke taka leda a Arsenal, Laurent Koscielny ya ajiye takalma buga wasansa na kasa da kasa bayan da ya gaza samun damar halartar gasar cin kofin duniya, da Faransan ta lashe na shekara 2018 wanda ya gudana a Rasha.
Dan wasan Koscielny, mai shekaru 33, da haihuwa ya yi matukar sa ransa wajan halartar gasar ta cin kofin duniya, amma aka cire sunansa daga tawagar 'yanwasan kasar faransa kar kashin jagorancin mai horas da ita Didier Deschamps, sakamakon raunin da yake fama da shi a kafarsa.
Bayan haka danwasan ya bayyana bacin ransa sosai na rashin kasancewa cikin tawagar Faransa, wace ta lashe kofin na duniya, inda ya kara da cewa hakan ya fi bakanta masa rai fiye da raunin da yake fama da shi.
Koscielny ya soki kocinsa, Deschamps kan yadda yayi watsi dashi na halin ko in kula a yayin da yake faman jinya, in da ya ce, sau daya kacal kocin ya kirashi ta wayar tarho don ya tayashi murnar bikin zagayowar ranar haihuwarsa a watan Satumba da ta gabata.
Koscielny ya ce, bama Didier Deschamps, ne kadai yayi watsi dashi ba dama daga cikin mutane sun yi watsi da shi a yayin zaman jinyarsa. “Yace ya lura cewa haka jama'a suke Idan kana cikin koshin lafiya, to zaka samu abokai da yawa, amma idan ka samu rauni, sai kaga an mance da kai bayan wani karamin lokaci.”
Danwasan ya buga wasanni 51 wa kasar Faransa, wasansa na karshe a Faransa shi ne a watan Maris wasansu da Rasha inda suka samu nasara daci 3-1.
Facebook Forum