A yayin da kungiyoyin kwallon kafa suke kokarin ganin sun nemi 'yanwasan da zasu saya don gyara kulob dinsu a watanJanairu mai zuwa.
Rahotanni na nuni da cewa dan wasan gaba na Manchester United Anthony
Martial, mai shekaru 22, a duniya ya shirya don watsi da tayin da kungiyoyin suke masa na sha'awar sayensa, irin Kungiyar Juventus, Paris St-Germain da Bayern Munich don ci gaba da zamansa a kulob dinsa.
Manchester City suna la'akari da matsayi dauko danwasan baya na Juventus dan kasar Brazil maisuna Alex Sandro, 27 da haihuwa. Kungiyar Juventus za ta kara da Chelsea wajan zawarcin matashin dan wasa mai shekaru 18 dan kasar Italiya maisuna Sandro Tonali, da zaran an bude hada hadar saye da sayarwa a watan Janairu mai zuwa.
Kungiyoyin Wolves, Leicester City, Southampton da kuma Fulham
ana danganta su da zawarcin dan kasar Portuguese mai shekaru 25 da haihuwa dan wasan tsakiya Joao Mario, wanda har yanzu bai taka leda wa Kungiyarsa ta Inter Milan ba a wannan kakar wasan bana.
Kungiyar Besiktas tace ba zata hana mataimakin mai horas da 'yanwanta
Guti ya koma Real Madrid ba, don maye gurbin Julen Lopetegui. Guti mai shekaru 41 da haihuwa ya kasance kusan shekaru 15 yana taka leda wa tawagar farko na Real Madrid.
Kocin Chelsea Maurizio Sarri yace danwasan baya na kulob din Marcos Alonso, 27 na iya zama dan wasan baya mafi kyau gefen hagun-baya a duniyar kwallon kafa, bayan da mai tsaron baya dan kasar Spain ya sanya hannu a sabuwar kwantiraki a Kungiyar ta Chelsea.
Facebook Forum