Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Iska Ake Daukar Cutar Hangum


Ciwon hangum wani ciwo ne da ke shafar kuncin mutum, wanda kuma ke janyo kumburi. Kamar yadda likitoci ke fadi shi dai wannan ciwon yana shafar tsokar nama a habar mutum, kuma ana daukar shi ne ta hanyar wasu kwayoyi wadanda in ba a magance su ba za su iya janyo wasu cututtukan.

Ana iya daukar ciwon hangum daga wani mutum zuwa wani, wato yana yaduwa ta hanyar shakar kwayar cutar a iska ko musayar yawu, da dai sauransu.

Wannan cutar dai ana samun ta ne ta shakar kwayar cutar mai suna MUMS a turance, wadda ke haddasa zazzabi mai zafi tana kuma shafar manya har ma da yara.

Malama Hurera, wadda dan ta dan shekaru uku da haihuwa ya kamu da cutar, ta fadi cewa ya fara da zazzabi ne da kuma kumburi a habarsa.

Malam Musa Mohammed Bello, kwararran likitan Iyali ne, yayi karin haske game da wannan cutar. Ya kuma ce cutar hangum na da alaka da wani bangaren tsokar nama dake jikin gabar dadashi, ko habar kasa wadda ke taimakawa wajen fito da yawu don narkar da abinci.

Likitan Ya cigaba da cewa cutar na yaduwa sosai ta hanyar iska, shi ya sa idan a gida akwai yara, ‘yan kasa da shekaru 6, da zarar wani ya kamu da cutar sai sauran duk su kamu. Likita Musa kuma ya bukaci iyaye su kai yaransu asibiti da zarar sun ga alamomin kumburi da zazzabi tattare da yaran nasu domin kare yaduwar wannan cutar.

XS
SM
MD
LG