Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Takaici Tsaffin Mawaka Su Shiga Kishin Masu Tasowa - Lizzy


Elizabeth Akinbo
Elizabeth Akinbo

Elizabeth Akinbo, wadda aka fi sani da Lizzy kin' ta ce babban abinda ke ci mata tuwo a kwarya shine yadda wasu mawaka ke neman cutar da wasu mawaka ‘yan uwansu mussaman a sakamakon karbuwar da suka samu cikin sana’ar su ta waka, mafi yawancin lokuta sai ka ga wadanda suka dade a harkar amma suna nema su yi kishi da masu tasowa.

Ta ce a farkon shigowarta harkar waka ta fuskanci matsaloli da dama daga wadanda suka dora ta akan hanyar sana’ar waka..

Lizzy kin, ta ce a iya saninta ta gaji waka ne, daga mahaifiyarta wacce mawakiyace irin ta kungiyar masu waka a coci inda daga nan ne ta koyi waka har ta mayar da ita sana’a

Ta kara da cewa waka wata hanya ce mafi sauki da Mawaki ke iya isar da dukkunin sakon da yake son isarwa – ta ce tana hallarta tarukan nishadantarwa ne ba da zummar tara dukiya ba, illa domin cika burinta a harkar ta waka.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:52 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG