Bada tazarar haihuwa muhimmin abu ne a bangaren lafiya musamman ga mahukunta, da kuma sanin lafiya da bukatar tsare-tsare a tsawon shekaru masu zuwa.
Ana fahimtar da tsarin tazarar haihuwa ne ta la’akari da alkaluman mace-macen mata yayin haihuwa ko mutuwar yara kanana.
Hukumar kiwon lafiya tace haihuwa ba tare da bada tazara ba babban kalubale ne dake fuskantar kiwon lafiyar bil’adama musamman lokacin da ba a samun abincin da jiki ke bukata.
Binciken baya-bayan nan da majalisar tayi ya nuna cewa mata da yawa na muradin yin amfani da abubuwan tazarar haihuwa amma basa samun haka, saboda rashin bayanai da kuma ayyukan kiwon lafiya, ko kuma rashin samun goyon baya daga mazajensu da ma al’ummar da suke zaune a cikin ta.
Malam Mohammed Ibrahim kwararren likitan mata ne, yace bada tazarar haihuwa na da muhimmanci kwarai don tabbatar da koshin lafiyar uwa da danta. Hakan zai taimaka wajen rage cututtuka kamar ciwon yunwa da ke samun yara, zai kuma rage hadarin kamuwa da cututtuka da suka shafi bangaren tsabta.
Malam Mohammed Yusuf, masanin halayyar dan’adam ne daga Kwalejin Ilimi ta birnin tarayya Abuja, yace “da haihuwar yu-yu-yu gara daya kwakkwara”. Ya fara da wannan karin magana ne a lokacin da ya ke bayani akan hakkin iyaye akan ‘ya’yan su. Malam Yusuf ya kuma ce rashin bada tarbiya mai kyawu ga yara na iya haddasa matsalar shaye-shaye ko dauke-dauke.
Shi kuma malam Aminu Ibrahim Daurawa, kwamandan hukumar Hisba na jihar Kano a lokacin da yake tsokaci dangane da matsayin tazarar haihuwa, cewa yayi da addini yace ayi aure a hayayyafa Annabi Mohammadu (SAW) zai yi alfahari da hakan ranar al-Kiyama, ai ba zai yi alfahari da yawan yu-yu-yu marasa amfani ba.