Fim din Akshay Kumar, wanda aka dade ana jira ya fito wannan jumma’ar a gidajen fina finai a kasar Indiya, bayan da a can baya aka dage nuna fim din domin baiwa fim din Sanjay Leela Bhansali, mai suna Padmavat, damar cin kasuwar ranar bikin zagayowar kasancewar kasar Indiya jamhuriyar.
Fim din na Akshay Kumar, wanda aka shirya akan yadda ake tsagwamar mata a kasar Indiya bisa batun jinin alada, daga dukkan alamu fim din ya samu karbuwa a wajen jama’a ganin cewa dama Akshay Kumar ya kasance mai yin fina finai dake da tasiri ga rayuwar mutane.
Wannan fim lalle ya bayana irin yadda ya kamata maza su kula da rayuwar mata, ba a ganinsu tafkar abun kyama ba idan suna alada kamar yadda yake a wurare da dama a kasar ta Indiya.
A baya ya fitar da wani fim mai suna Toilet Ek Prem Katha, fim din da ya tabo batun yadda jama’ar kasar ta Indiya, ke yin bayan gari a wuraren da basu dache ba. Ganin cewa shahararen jarumin na Bollywood, baya ga ankarar da jama’a akan sakonin da yake son mikawa ga jama’a haka kuma yana da dabarun nishadantar da jama’a a cikin fina finan sa.
Ganin irin wannan kokori da jarumin ke yi a fina finansa a cewar wadanda suka kalli fim din a ranar farko sunce lalle ya cancanci a yaba meshi, inda suka ce ya tabbatar jan gwarzo a Bollywood.
Facebook Forum