Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Bukatar Gwamnati ta Tallafawa Masu Sana’o’in Hannu


Sana’a ko kasuwanci na da muhimmanci a rayuwar kowacce al’umma don iya dogaro da kai da kuma raya al’umma baki daya.

Wata matashiya mai suna Asabe Usman, da ke da zama a garin Jos na Jihar Filato, ta ce kwangilar dafa abincin bukukuwa, da hada sarkoki, ‘yan kunnaye da awarwaron duwatsun mata har ma da wanda maza za su iya sawa su ne sana’o’in da ta ke yi. Tana kuma yin gurasar nan da ake kira cake a turance.

Da wannan sana’ar, Asabe na samun riba daidai gwalgwado musamman in ta sami kwangilar dafa abinci. Asabe ta ce albarkacin sana'ar da ta ke yi, ta na samun dan abin kashe duk wata wuta da ka iya tasowa. Ta kuma ce tana tallafawa maigidanta da sauran ‘yan uwa idan da bukatar yin hakan.

Kusan kowacce sana’a ta na da tata ribar amma adana ribar ya kan zama da matsala. Matashiyar ta ce ta bude asusu a banki, duk ‘yar ribar da ta samu sai ta garzaya banki ta je ta ajiye.

Asabe Usman kuma ta yi kira ga gwamnati da ta cigaba, ko ta kara akan tallafin da ta ke badawa ga masu sana’ar hannu musamman ta bangaren kudin jari. Bayan haka zai kyautu gwamnati ta hana shigar da wasu kayayyakin daga kasashen waje, don na gida su samu su shigar da nasu.

XS
SM
MD
LG