Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Sauran Aiki a Gaban Chelsea


Chelsea
Chelsea

Biyo bayan nasarar da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, ta samu akan Manchester United, a wasan da suka yin a stamford Bridge, a jiya, inda Manchester ta sha kashi da ci daya mai banhaushi, yasa yanzu kungiyar ta Chelsea, tana kan gaba da ratar maki goma.

Eden Hazard, wanda ya jefawa Chelsea kwallo a ragar Manchester United, ya gargadi ‘yan kungiyarsu da kada suyi kasa a gwiwa duk da ganin cewa sun dare samman teburin frimiya lig.

Inda har Chelsea, tayi nasara lashe kofin na frimiya lig, wannan shine zai kasance karo na farko a cikin shekaru biyar da zata lashe kofin.

Hazard, ya cigaba da cewa abun farin ciki ne doke Manchester United, kuma a filin wasa na Stanford Bridge.

Ya kara da cewa an kusa kaiwa ga nasara amma akwai sauran aiki domin sai sun lashe wasani biyu na gaba.

XS
SM
MD
LG