Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alkali Ya Yanke Mata Hukuncin Rataya


Mai Shari'a a babbar Kotu a jihar Bayelsa Mr Nayai Aganaba ya yanke wa wata mata Victoria Gagariga ‘yar shekaru 30, hukuncin kisa ta rataya.

an kama Victoria da laifin kashe mijinta, Henry Gagariga, ranar 4 ga watan Feburairun shekarar 2013, a gidan su da ke kan hanyar Ebisam a Afenfa, dake birnin Yenagoa, a jihar bayelsa.

Yayin da mai sharia ke karanta hukuncin wanda aka kwashe tsawon shekaru uku ana tafka shari’a, Aganaba ya ce masu sauraron shari’ar sun kira shaidu shida, kuma sun gabatar da shaida yayinda da wacce ake zargin ta samar da shaida guda daya kacal.

Mai Shari’ar ya ce dukkan shaidun da masu shigar da kara sun gabatar da shaidun a gaban kotu kuma duk sun nuna cewa wace ake zargi ta aikata laifin.

Ya kara da cewa shaidun da aka gabatar sun nuna cewa tunanin mutum dole ya bayyana masa cewa tabbas ita ce kadai tare da mijinta, mamacin a lokacin mutuwarsa, kuma ita kadai ke da damar kashe shi bisa shaidar da aka kawo kotu.

Mai shari’a ya cigaba da bayani inda ya ce Victoria ta aikata kisan da son ranta wanda ya jibanci kishi saboda ita da mijinta suna kazamar kaunar juna tsakanin su.

Zan bayana hukucina, a cewar alkalin Na yanke hukuncin kisa ta hanyar ratayar wuya har sai kin mutu. Allah ya gafarta miki.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG