Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amuneke Yace an yi Karon Batta Sosai


'Yan Kwallon U 17
'Yan Kwallon U 17

Kwach Emmanuel Amuneke mai koyar da ‘yan wasan Golden Eaglets na Najeriya ya bayyana farin cikin cewa yaran nasa ‘yan kasa da shekara 17 sun samu tsallakewa zuwa ga wasan karshe na gasar cin kofin duniya da ake yi a kasar Chile, a bayan da suka yi waje-rod da ‘yan kasar Mexico da ci 4 da 2.

‘Yan Golden Eaglets, wadanda ke rike da wannan kofi a yanzu haka, zasu fuskanci zakarun gasar ‘yan kasa da shekara 17 na Afirka, Mali a wasan karshe da za a yi ranar lahadi.

Amuneke yace an yi karon batta sosai domin dukkan kasashen biyu sun yi bakin kokarinsu. Mun jinjina ma Mexico saboda kwarewarsu da kuma jajircewa. Ya fadawa shafin inatnet na FIFA.COM cewa sunyi farin cikin shiga wasan karshe domin kare wannan kofi nasu. Mali tana da karfi, ita cde zakarar Afirka. Za a buga tamaula sosai.

Kwach na ‘yan wasan kasar Mexico, Arteaga, ya dora laifin kashin da suka sha a hannun Najeriya kan yadda ‘yan wasansa suka kasa kammala wasannin da suke farowa idan sun koro kwallo. Yace da ma mun san za a yi karon batta, kuma wasan zai zama mafi tauri ma a duk wannan gasa ta cin kofin duniya. Amma abin takaici, ba mu iya mun jefa kwallayen da suka kamata a raga ba. Sai dai, da ma haka kwallon kafa ya gada. Mun so muje wasan karshe, amma tun da ba mu samu zuwa ba, yanzu zamu mayar da hankulanmu a kan wasan neman matsayi na uku, in ji shi.

XS
SM
MD
LG