Cikin wannan makon ne babbar cibiyar da ke kula da lafiyar motoci ta Amurka ta ci kamfanin Takata da ke sarrafa jakar iska ta mota, na kasar Japan tarar dala miliyan 200 don kasa gargadin jama’a da gwamnati da yayi akan yadda jakkar iskar ke fashewa.
Mutane 7 ne suka mutu kuma kusan 100 suka jikkata a lokacin da jakar iskar, da aka yi su musamman don kare matukin mota da pasinjoji a lokacin hadari, ba zato ba tsammani ta ke fashewa, tare da watsa barbashen karafuna da gilashi ga kai da jiki.
“Shekaru da dama ke nan da kamfanin Takata ya kera, da kuma saida kayayyki masu illa, amma kamfanin ya ki ya yarda da illar kayan, kuma ya kasa ba hukumar da ke kula da harkokin sufuri ta manyan titunan kasar Amurka, ko masu yin amfani da kayayyakinsa da ma sauran jama’a cikakken bayanin damejin”, a cewar sakataren hukumar Anthony Foxx.
Duk a cikin matakin da aka dauka, kamfanin zai daina sarrafa, tare da saida jakkunan iska da aka yi amfani da iskar ammonium nitrite, abinda kwararru ke gani yana daya daga cikin dalilin dake sa fashewar jakkar.
Kwararru masu kula da lafiyar mota da direbobi na kyautata zaton cewa akwai miliyoyin motoci a fadin duniya da ke dauke da wadannan jakkunan masu dameji a cikin motocinsu.