Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cafke Wasu Barayin Shanu An Kuma Kwato Shanu


Shanun Fulani.
Shanun Fulani.

Rundunar 'yan sandan jahar Sokoto, ta kwato Shanu 80, daga hannun wasu barayin Shanu su uku wandada yanzu ke hannun hukumar a jahar.

Kakakin rundunar 'yan Sandan jahar Mr.Sabo kurawa, wanda ya tabbatar da lamarin ga manema labarai ya ce 34, cikin Shanun na wani mutun mai suna Lawali Gidan Igwai, ne.

Ya ce Lawali ya kai rahoto ga 'yan Sanda cewar wasu mutane uku sun yi masa fashin Shanun sa a lokacin da yake kiwo a kauyen Birisawa a karamar hukumar Tureta.

Daga samun rahoton sai 'yan Sanda da taimakon 'yan kato da gora suka yiwa dajin kawanya Allah kuma ya basu sa'ar kwato Shanu 34, a cikin 46, da suka sace daga gareshi.

Mr. Kurawa, ya ce 'yan Sanda kuma su samu wasu Shanu a daji babu makiyayi, yana mai cewa ana tsammani cewa barayi ne suka sake su a dajin.

XS
SM
MD
LG