Bayan bayyana dage zabe mai zuwa da hukumar zaben Najeriya, tayi, al’uma, da kungiyoyi masu zaman kansu na cigaba da bayyana ra’ayoyinsu, game da wannan sabuwar mataki da hukumar ta dauka.
A jihohin Borno da Yobe dai, da rigiggimun Boko Haram, ya yiwa katutu na gaba-gaba wajen bayyana ra’ayoyinsu, game da matakin da hukumar ta dauka na dage zaben, sakamakon batutuwan tsaro da tace tana fama dashi.
Wani Malam Ishaq, daga jihar Borno, yace”Kowa ya dauka tundun muntsirar mu shine aiwatar da zaben, kuma tsammanin da muka say a tafi gaba, toh da gaban da yanzu duk kadarar Allah ne sauki kuma daga Allah ne.”
Shi kuwa Malam Zakari Adamu, daga jihar Yobe cewa yayi “ Wannan dage zaben da akayi mu bai zo mana da mamaki ba, don dalili abune wadda an dade ana shirya wannan makircin.”