Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Dakile Cutar Shan Inna Ko Polio A Najeriya


Yau a fadar gwamnatin Najeriya, shugaban kasa yayi wata ganawa ta musamman da jami'an da ke kula da sha'anin kiwon lafiya bakidaya na Najeriya ciki harda kasaitattun attajiran nan Mr Bilgate da Aliko dangote wadanda suke tallafawa Najeriya wurin yaki da cututtuka dake addabar al'uma musamman ciwon nan na shan inna da wasu cututtuka dake shafar kananan yara.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ji dadi kwarai kuma ya yaba da cewar yanzu babu sauran wani yaro ko yarinya dake dauke da cutar shan inna ko polio a kasar bakidaya a cikin watanni goma sha takwas da suka gabata.

Bayan kammala taronne wakilin sashen Hausa Umar Farouk Musa ya tattauna da Dr Ado muhammed babban sakataren hukumar kiwon lafiya mataki na farko a Najeriya domin jin yadda ganawar su da shugaban kasa ta kaya.

Likitan ya bada bayanin cewar ganawar ta su tayi kyau sosai domin kuwa wannda yafi kowa kudi a duniya da kuma wanda yafi kowa kudi a Afirka sun halarci ganawar kuma sun ziyarci shugaban kasa inda suka taya shi murna da kuma yaba mashi kan wannan gagarumar nasara da aka samu ta kawar da cutar shan inna da aka fi sani da polio a Najriya.

Ga cikakken rahoton...

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG