Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Damke Dan Shekaru 13 Dan Kungiyar Asiri


Jami'an Civil Defense
Jami'an Civil Defense

Jami’an Civil Defense reshen jihar Nasarawa a tarayyar Najeriya, ta damke wani matashi mai shekaru goma sha uku wanda ake kira “Touch and See” a yankin Shange a karamar hukumar Lafia.

Shi dai wannan matashi ya na cikin gungun wasu ‘yan kungiyar asiri ne wadanda aka dade ana farautarsu.

Kwamandan Civil Defense na jihar ta Nasarawa Muhammad Gidado Fari, wanda ya bayana matashin da kuma wasu masu laifi da suka hada da barayi, da masu zamba cikin aminci, yace rundunar na bukatar taimako daga jama’a, wajen domin hannu daya baya daukar jinka.

Rundunar ta damke mutane ashirin da shida da ake zargi da laifuffuka daban daban a jihar ta Nasarawa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG