Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Gardama akan Harin Zamfara - 13/4/2014


Mutanen da aka kashe a jihar Zamfara, lokacin da ake yi musu jana'iza, 6 ga Afirailu 2014.
Mutanen da aka kashe a jihar Zamfara, lokacin da ake yi musu jana'iza, 6 ga Afirailu 2014.
NAJERIYA - Sanata Dansadau daga jihar Zamfara yayi tsokaci akan kisan da akayi a jihar, makonnan ya wuce. Sanata Dansadau yace “kawai suka zo, suka kama harbin mutane. Abunda ya tayar mana da hankali shine, a madadin hukuma ta tausaya mana, an ce a’a, wai muke da laifi.”

NAJERIYA - Amma komishinan ‘yan sandan jihar, Ibrahim Birnin Magaji ba haka yake ganin lamarin ba “su kansu, gwamnoni na wadannan jihohi, Kaduna da Neja, da Kebbi, suma Sa’idu Dansadau yaci amanarsu domin mutanensu ne ya dauko aka zo, aka yi wannan taro, ba tare da sanin hukuma ba.”

NAJERIYA - Kalamin Malam Ibrahim Shekarau dan PDP dangene da jihohin dake fama da rigingimu ya bar baya da kura, inda yace kar ayi zabe a 2015. Malam Ahmed Sajo shine darektan yada labaran gwamnan Adamawa Murtala Nyako “abunda dai, abun takaici ne. Shi maigirma Ibrahim Shekarau idan ka lura kwanan baya da yazo nan Adamawa, mu karrama shi, mun mutunta shi.”
XS
SM
MD
LG