Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Gurfanar Da Amurkawan Nan Masu Niyar Shiga Kungiyar ISIS Gaban Kotu


Dan kungiyar ISIS
Dan kungiyar ISIS

'Daya daga cikin mutanen da ake tuhuma a jihar Minesota ta Amurka, da yunkurin zuwa Syria domin shiga kungiyar ISIS ya amsa laifin sa jiya a kotu.

Abdul razak Mohammed Warsame, yana cikin mutanen nan biyar ‘yan Minesota wadanda suka shirya tafiya Syria a ciki shekarar 2014 domin shiga cikin kungiyar ISIS.

Suma sauran 4 za a gurfanar dasu a cikin watan Mayu.

Babban mai gabatar da kara yace wadannan mutanen sunyi kokarin ficewa daga Amurka, ta barauniyar hanya ba tare sanin jami'an shige da fice na Amurka ba domin gudanar da wannan tafiyyar da suka kudiri aniyar yi.

Mahukuntar kasar Amurka suka ce birnin Minnesota na daya daga ciki manyan biranen dake da musulman ‘yan gudun hijira daga Somalia, kuma yanzu haka ana kara samun masu tsananin kishin addini wadanda suka ce suna iya rikidewa su zame ‘yan ta'adda.

Babban mai shari'a na kasar Amurka reshen jihar Minnesota Andrew Luger yace tuni kungiyar ISIS tadade tana neman wadanda zata horas domin shiga cikin kungiyar ta kuma wannan ba sabon abu bane.

XS
SM
MD
LG