A cewar daya daga cikin kafafen yada labarai na Taiwan News, an fitar da daya daga cikin alamomi 40 da akayi na mutane a fitulun bada hanya don baiwa ababen hawa umurni a kan hanyoyi, da nunama matafiya a mota ko akafa ka’idoji da suka kamata subi. An bayyanar da wadannan sababbin alamomin ne a wani taro na musamman yau, a kudancin karamar hukumar Pingtung.
Alamun mutane biyun da akayi na tsallaka titi na nuna hoton namiji ya duka yana rokon budurwar shi data aure shi, sai kuma koren na miji yana rike da hannun budurwar suna tsallaka titi.
Jami’an ‘yan sandan yankin sun baiwa zanen lokacin gwaji a watan Disambar da ta gabata, daga bisani kuma suka bayyanar da kudurin su na maida zanen ya zama alamar tsallaka titi a fadin kasar a shekarar nan ta 2018 domin sabuntawa da kayatar da alamun tsallaka titin da suka kai shekaru 18.
Magajin garin Pingtubg Pen Men-an, ya shaidawa kafar yada labaran Taiwan cewar, zanen zai shaidawa mutane cewa Pingtung gari ne mai cike da soyayya. Wanda yayi zanen ya shaidawa kafar yada labaran Apple, fatan shi na zanen ya zamo abinda zai ja hankalin matasa domin su kiyaye harkokin zirga zirgar su.
Facebook Forum