Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Shi Saboda Budurwa


An kashe wani dalibin jami’ar , a Dutse babban birnin jihar Jigawa , Bashir Musa, biyo bayan wata rashin jituwa kan budurwa.

Rikici dai ya kwaure ne a lokacin da budurwar mamacin Aisha Sale, daliba a Polytechnic din jihar Jigawa, wace kuma ake zargin cewa tana da wasu samari har 6, daban a makarantar da Bashir Musa, yake.

Bayanai sun ce Musa, dai ya samu labarin cewa budurwarsa ta kaiwa wani saurayi ziyara sai shi da wasu abokansa suka nufi gidan daga bisa sai fada tsakaninsu wanda ya jawon mutuwa Musa.

Da yake bayani akan magatakardan makaratar Malam, Yusuf Adamu, ya ce jami’ar zata fida bayani amma sai baya ‘yan Sanda sun gama bincikensu.

Kakakin ‘yan Sandan jihar DSP Abdul Jinjiri ya tabbatar da afkuwar lamari.

XS
SM
MD
LG