Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rufe Makaranta Domin Zargin Maita


Hukumomin wata makaranta a yankin Chivi, dake kasar Zimbabwe sun rufe makarantar har sai illa masha Allahu biyo bayan zargin maita a makarantar.

Ganin yadda daliban makarantar ke suma hakannan babu dalili kamar yadda wata mujallar kasar mai suna Zimeye, ta ruwaito tace daya daga cikin mahaifan daliban wanda bai so a ambaci sunansa ba ya danganta abinda ke faruwa a makarantar da maita dakuma mugayen iskokai.

Mujalllar ta kara da cewa abubuwa na ta faruwa a makarantar na ban mamaki kamar yadda wata yarinya ‘yar aji biyu tayi dogon suma mai tsawon gaske tafkar ta bar duniya.

Kansilan a al’umar Chivi Wilson Machingambi, ya shaida cewa iyaye da dama dasuka fusata sun cire ‘ya’yansu daga makarantar wanda hakkan yayi sanadiyar hukumomi suka rufe makarantar.

XS
SM
MD
LG