An samu shahararren dan wasan gudun kasar Afirka ta Kudu, Oscar Pistorius da laifin aikata kisa, amma an wanke shi daga aikata wasu laifuffukan kisan kai mafiya girma masu nasaba da mutuwar budurwar sa.
A yau Jumma'a mai shari'a Thokozile Masipa ta yanke hukuncin da aka dade ana jira a yankewa Pistorius, wanda ya kashe budurwar sa Reeva Steenkamp a gidan sa.
Masipa ta ce Pistorious bai yi tunani ba lokacin da yayi ta harbin kofar ban daki, bayan ya san cewa akwai mutum a ciki, kuma wanda ke ciki na iya mutuwa sanadiyar harbin da yayi, amma, yayi ne ba da niyya ba. Mai shari'ar ta ce lauyoyin gwamnati masu shigar da kara sun kasa nuna shaidar cewa da gangan, da niyya Pistorius ya aikata kisan. Ta ce ba za a iya cewa ya aikata laifin kisan kai da gangan ba, amma, ya aikata laifin kisa. Kenan maimakon daurin shekaru ishirin da biyar ko fiye da haka a kurkuku, yanzu zai iya yin shekaru goma sha biyar a gidan kaso sakamakon samun sa da laifin aikata kisan mutun.