Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An yi Bukin Yaye Wasu Matasa da Suka Koyi Sana'ar Hannu a Jihar Neja


Sana'ar Hannu
Sana'ar Hannu

An gudanar da wani gagarumin bukin yaye wasu matasa maza da mata da yawan su ya kai 2000, da suka koyi sa’o’in hannu daban daban a jihar Neja.

Matsalar rashin aikin yi na daya daga cikin matsalolin da suka addabi ‘yan Najeriya musamman matasa. Gwamnati jihar ta ce ta kashe sama da naira miliyan 680 wajen horar da wadannan matasan tare da samar masu kayan aiki da zasu fara yin dogaro da kansu, a karkashin shirin nan na cire kudaden man fetur da ake kira “Sure P” a Najeriya.

Alhaji Hassan Nuhu, shine babban daraktan kula da wannan shiri a jihar Neja. Ya fadi cewa manufar su ita ce ganin matasa sun sami aikin yi, da yakar talauci da kuma kara samun tsaro da zaman lafiya a kasa.

Malama Amira Aliyu na daya daga cikin wadanda suka koyar da matasan, tace suna binsu ne a yankunan karkara domin koyar da su, amma sun fuskanci matsalar ganawa da wasu, saboda banbancin harshe da aka samu.

Hajiya Aisha Babangida, da ita ma tana da wani shirin tallafawa matasa ta halarci wannan taron, ta kuma yi kira ga matasan da su tashi tsaye, su kuma yi amfani da wannan damar da suka samu don kada a bar su a baya.

XS
SM
MD
LG