An yi lalata da yara sama da 500 a wata makarantar koyon wakokin coci mallakar majami'ar Katolika a kasar Jamus a tsakanin shekarar 1945 zuwa 1992, a cewar wani rahoton da aka fitar yau Talata.
Wani rahoton lauya Ulrich Weber, ya nuna cewa wasu mutane 49 sun yi lalata da yara maza akalla 547 a shahararriyar makaranatar koyon wakoki ta Domspatzen.
Weber, wanda ya fara bincikensa a 2015, bayan da aka sa shi binciken sanadiyyar wata tabargzar lalata ta 2010 da ake zargin wasu 'yan Katolikan da yi, ya ce wadanda abin ya rutsa da su kan fuskanci abin da ya kira, "tashin hankali, da tsoro da kuma rashin mai taimako" sannan makarantar kan zame masu tamkar "ursuna, gidan bala'i ko kuma wani abu mai kama da inda aka taba tara Yahudawan da aka hallaka."
Weber ya ce al'adar nan ta yin gum ta taka rawa wajen lalatar, sannan ya yi nuni da wani tsohon mai koyar da wakar ko choir master mai suna Georg Ratzinger, wanda ya jagoranci koyar da wakokin daga 1964 zuwa 1994, wanda Weber ya ce dole a tuhume shi da laifin kawar da kai yayin da ake aikata aika-aikar.
To amma Ratzinger, wanda dan'uwa ne ga tsohon Paparoma Bemedict, ya ce sam shi bai taba sanin aukuwar haka yayin da ya ke shugabantar wurin ba.
Facebook Forum