Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yiwa Hukumomin Kasar Nijar Hannuka Mai Sanda Da Wakar Tayi Tauri


Wasu matasan mawaka a jamhuriyar Nijar, karkashe jagorancin, Idi Sarki, sun fito da wata sabuwar wakar mai taken ( TAYI TAURI) dake hannunka mai sanda ga ‘yan siyasa saboda yadda ake zarginsu da yin fatali da tarin matsalolin dake addabar talakkawa shekara da shekaru yayinda ake ganin ‘yan siyasa musamman masu mulki suke azurta kansu ta barauniyar hanya.

Wakar da Idi Sarki, da hadin guiwar takwarorinsa na M.D crew, suka rera a halin yanzu ita ke tashi a kasar ta jamhuriyar Nijar, saboda yadda wakar ta samu karbuwa a tsakanin matasa da sauran al’umar gari.

Ita dai wannan wakar ta fayyace a zahiri halin da talakawa ke ciki ne a kasar ta Nijar, daga 1991, kawa yau.

Idi Sarki, yace makasudin yin wannan wakar shine domin sun ga cewa kawo yanzu babu abinda ya sauya, duk da irin arzikin ma’adanai da Allah, ya horewa kasar.

Aiyukan rusau da hukumomin Nijar, suka kaddamar a watan Agustan, da ya gabata a wasu biranan kasar inda duban shaguna na matasa suka salwanta akan hujjar gyaran gari, shine abinda ya yiwa wadannan mawaka matashiya domin rera wakar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00

XS
SM
MD
LG