An gudanar da wani taron sa hannu a yarjejeniyar zamanlafiya a lokacin zabe, da kuma kara wayar da kan Matasa da ma Al’umah baki daya, dan gane da hanyoyin da za’abi don gujema hadduran dake cikin amfani da kudi ko matasa lokacin zabe don tada zaune tsaye.
Wannan taron da aka gudanar a garin Kwantagora jihar Naija. yasamu halarta wasu ‘yan siyasa, shuwagabanin addinai, jami’an tsaro da ma al’uma baki daya. Mahalarta wannan taron dai sunyi tsokaci kamar haka. Dr. Aliyu Sabi Abdullahi, Baraden Bargu, kuma dan takarar kujerar sanata a jihar Naija. Yayi kira da cewar baki daya al’uma a gujema tada hankulla don wannan ba zai kai kasar ga cigaba ba, idan har babu zaman lafia a tsakanin al’umah to babu wani cigaba da za'a samu, yace wannan lokacin zaben yana daga cikin abun da kowane dan Najeriya ke so ya gani, don mahimanci wannan lokacin.
Shima Alh. Usman Magaji Tafidan Nasco, yayi kira da jama’a su guji bangar siyasa musamman ma matasa da ake amfani dasu wajen muzgunama jama’a don wannan kawai zai gurgunta tsarin demokaradiyane, idan akace baza ayi abun da yadace ba, kuma yakamata mutane su yi kokarin bin doka da oda.
A ta bakin Malam. Aliyu Sani Adarawa, shugaban majalisar malamai ta kungiyar IZALA, yayi kira da jami’an tsaro su guji muzguna ma al’uma don kyautatama wasu tsurarun ‘yansiyasa don wasu abubuwa da zasu iya basu, yace so da dama akanyi amfani da jami’an tsaro wajen yin magudin zabe da kuma murkushe cigaban kasa, duk dai sunyi nuni da cewar wannan bai kamata ba.