Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zargin Jarumi Morgan Freeman Da Aikata Masha'a


Morgan Freeman
Morgan Freeman

Ana zargin shahararen tauraron dan wasan film din Amurka, kuma fitacce a Hollywood, wanda kuma ke bayar da agaji a fadin duniya, Morgan Freeman, da cin zarafin mata.

Yanzu haka cikin mutane 16 da suka yi magana da kafar yada labarai ta CNN, mata 8 sun tabbatar da cewa ya ci zarafin su tun daga lokacin da ya fara sana’arsa ta fim kuma shaidu 8 sun tabbatar da aukuwar wannan lamari.

Wata mai bada umurni ta ce a shekarar 2015 ta yi aiki da Morgan Freeman, yayin da ake shirin wani fim na ban dariya da ya fito a ciki mai suna, 'Going in Style', ta ce Morgan ya yi ta cin zarafinta, inda ta zargi Freeman da tabata ba sau daya ba kawai ba tare da izininta ba. Haka kuma ya sha yin furuci kan shigar suturarta da yanayin surarta.

Ta ce “akwai wani lokacin ma da yayi kokarin cire min siket, yana tambayata ko na saka pant, amma bai samu sa’a ba. Na ce masa ya bari, sai ya firgita ya rasa abin da zai ce”.

Wata furodusa a wani fim din da aka shirya mai suna, 'Now You See Me' a shekarar 2012, ta fadawa CNN cewa Freeman, ya sha yin magana kan surarrsu. Ya sha fada masu cewa, su daina saka riguna da za su nuna surarsu, ma’ana karsu saka matsatsun kaya.

CNN ta nemi jin tabakin shahararren dan wasan akan jerin zarge zargen da ake masa amma bai bada amsa ba. Wani mai daukar rahotonnin Hollywood yayi kokarin samun Freeman amma ya ci tura.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Hafsat Muhammed

    Hafsat Muhammed, Ma’aikaciyar Jarida ce (International Broadcaster - Multimedia) a Sashen Hausa na Muryar Amurka dake birnin Washington, D.C.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG