Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Anya 'Yan Gidan Khan Zasu Iya Doke Akshay Kumar A Bollywood Kuwa!


Akshay Kumar
Akshay Kumar

Tarihi ya nuna cewa Salman Khan, Shah Rukh Khan da Aamir Khan a shekaru goma da suka wuce fina finan su na tasiri a Bollywood, inda suke samun makudan kudade a duk wani fim din da suka fitar wadanda ake nunawa a gidajen kallon sinima a kasar Indiya.

Amma a ‘yan shekarun baya bayan nan Akshay Kumar, ya yunkuro a fina-finan da yake shiryawa inda duk fim din da yayi kan samu karbuwa ta inda yake tabbatar da cewa wadanda suke ma’amala da fina-finan suma sun maida kudinsu.

A fim din Akshay Kumar na baya mai suna Jolly LLB2, ya kai fim din kololuwar da ake ganin cewa abinda kamar wuya Salman, Aamir da Shah Rukh Khan su iya doke shi.

Akshay Kumar, a yanzu haka yanada fina finai hudu masu suna Airlift, Housefull 3, Rustom da Jolly LLB 2, sun kuma samar masa da kudi har dala miliyan goma sha biyar (15,000,000) a cikin watani goma sha uku, (13).

Kuma ganin cewa Shah Rukh, Aamir da Salman sunce fina finai biyu ko uku zasu fitar a shekarun 2017 da 2018, idan dai a haka zasu tsaya to tabbaci hakika ba zasu kamo Akshay Kumar ba.

A bana Akshay Kumar zai fitar da fina finai hudu bayan Jolly LLB2, akwai Naam Shabana,Toilet Ek Prem Katha da 2.0, kuma da wadannan zai iya sake samun dala miliyan goma sha biyar (15,000) idan haka ya kasance sau bakwai a jere kenan yana samun dala miliyan goma sha biyar biyar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

XS
SM
MD
LG