Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta INEC Farfesa Attahiru Jega, ya maida martani ga masu kiran sa da yayi murabus. Inda yace, “Wa’adin aikina zai kare ne a watan Yuni na wannan shekarar, kuma ba wanda zaiyi min wata barazana kan na ajiye aiki, in abin ajiye aikin yazo zan ajiye.”
A cikin wadanda yake maidawa martanin cikinsu har da dattijon ‘yan Niger Delta, da shugaba Jonathan ke girmamawa Edwin Clark, rade radi dai sun fito a jaridun Najeriya dake zargin a kwai wani shirin cire Jega daga mukaminsa, sai a nada wanda zai zama ‘dan amshin Shata, haka nan tuni wadansu sun shiga babbar kotun tarayya don kalubalentar dan takarar adawa janal Buhari akan maganar takardarsa ta sakandare.
Shin Jega zai iya tsallake wannan siradin na samun gudanar da zaben ko kuwa za’a dage shi daga hukumar kamar yadda ya dage zaben? shin jami’an tsaro zasu iya kwantar da fitinar arewa maso gabas cikin mako shida? A binda da dai yazama zahiri shine sabanin magana, da farko aka daura bukatar dage zaben da rashin raba miliyoyin katunan rajistar zabe, inda daga karshe akace a’a maganar tsaro ce ta kawo cikas din.