Gwamnan Jihar Damagaran Kalla Moutari ya bayyanawa Halima Djimroa ta nan Muryar Amurka cewa a halin da ake ciki a yanzu ba su da bukatar kafa sansanin ‘yan gudun hijirar nan fiye da dubu goma da suka fito daga Jiha Diffa suka ratsa ta Jihar Damagaran. Yace basa bukatar yi musu matsuguni domin kuwa dangin ‘yan gudun hijirar da ke zaune a garin sun basu masauki da kulawa daidai gwargwado.
Sannan ya kara haske game da wadanda aka kama a cikin ‘yan gudun hijirar kimanin mutane ashirin da biyar bisa zargin cewa ‘yan ta’addar Boko Haram ne suka saje da ‘yan gudun hijirar. Inda yace ana zarginsu ne sannan kuma da zarar an tabbatar ba su da laifi to za a sallame su kamar yadda doka ta tanada.
A karshe yayi kirayi ga jama’a da su ba wa gwamnati cikakken hadin kai don kare rayuka da dukiyoyin jama’a don samun ci gaban kasar.