WASHINGTON, DC —
Hare-haren ta’addanci da tada boma-bomai a wuraren ibada, makarantu, kasuwani, tashoshin mota Bankuna da gidajen mutane, a arewacin Najeriya, a kullu yomin, alamu ne dake bayan gazawar Gwamnatin kasa a fanin tsaro.
Saboda haka ne yasa, Shahararren Shehun Malamin nan Dahiru Usman Bauchi, ya bukaci jama’a, dasu kare kansu.
Malamin ya furta haka ne a wani ganawa da yayi da manema labarai, a garin Bauchi, ciki harda wakilin muryar Amurka, Abdulwahab Muhammad.
Dahiru Usman Bauchi, yace akwai ‘yan Boko Haram din da aka nada, domin a cewar sa ‘yan Boko Haram din na asali su nawa ne kuma Sojojin Najeriya, su nawane, saboda haka Malam yace akwai lauje cikin nadi.