Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Binciken Masu Anfani Da Kwayoyin Kara Kuzari A Jahar Lagos


Babban daraktan wasanni na jahar Lagos Deji Tinubu yace gwamnatin jahjar na kokarin shirin samar da isassun kayan aiki ga bangaren lafiya wanda zai maiyar da hankali wajan gano masu wasan motsa jiki da ke anfani da magunguna masu kara kuzari.

A ranar Talata ne Tinubu ya bayyanawa jaridar New Nigeria (NAN) a birnin Lagas cewar akwai matukar anfani da kuma bukatar kawo karshen anfani da magungunan kara kuzari da wasu ‘yan wasa ke anfani da su.

Jami’in na gwamnatin jahar Lagos yayi bayani dangane da komabayan da kasar Rasha ta samu bisa ga dakatar da ita da kungiyar wasannin motsa jiki ta duniya ta yi a sakamakon zargin masu wasan motsa jikin kasar da aka yi da anfani da kwayoyin kara kuzari.

Jami’in ya kara da cewa “ muna da fanni na lafiya wanda muke sa ran nan da dan lokaci kankane zai fara gudanar da ayyukan binciken amfani da kwayoyi masu nasaba da kara kuzari a lokacin wasanni koda shike bazan iya tsayar da ranar da bangaren zai fara gudanar da ayyukan sa ba, amma nan da lokaci kadan zai fara aiki.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG