Shirin Bigg Boss, shiri ne mai farin jini a ciki da wajen Indiya, kuma ya samu karbuwa ga jama’a, wanda dalilin haka yasa yanzu ake kan gabatar da shiri na 9.
Wannan shine mako na 43, a shirin na Bigg Boss wanda yake a kowane mako akan bi sahun shirin aga yadda jama’a suka karbi shirin .
A wancan makon da ya gabata shirin ya tabuka abun arziki amma a karshen makon da ake sa ran cewa zai harba sama sai ya durkushe da kimanin kusan kashi 50 cikin 100.
Wanna ya jawo damuwa ga masu shirya shiri inda aka bukaci masu gabatar da shirin dasu kara nuna fasaha da bajinta domin habaka karbuwar shirin.
Koda yake a yankunan karkara shirin bai samu karbuwa ba wanda hakan ba zai rasa nasaba da ganin cewa akasarin mutanen karkara kan kali Talabijin ne har zuwa karfe 10 ko 10.30 na dare.
Kuma akwai damuwar cewa abubuwan da shirin ya kunsa abubuwa ne da bai dace ba ga iyalai.
Duk da yake ana ganin cewa lokaci da ake watsa shirin yayi dare akwai harsashen cewa masu gasar ma basu taimakawa shirin, ko shima Salman Khan, da yake sawa jama’a anashiwa shima akwai alamar gundura a fuskansa.