Idan har kuna biye da mu a tattaunawar mu da Malama. Shema’u, wadda suke da kungiya me kula da kananan kungiyoyi masu kokarin neman bashi don habaka sana’o’in su a kowane mataki. A wannan karon, tayi Karin haske kasan cewar ita dai kungiyar su tana, kokarin wayar ma jama’a kai ne don ta yadda zasu samu su karbi bashi daga hannun bankuna, da kuma yadda zasu yi amfani da wadannan kudaden don bunkasa sana’o’in su a ko ina.
Ta yi nuni da cewar wannan wata damace da babban bankin Najegeriya wato CBN ya fito da shi me suna MSDEF don bama masu karamin karfi damar gina kasuwancin su, ta karbar bashi da kuma hanyoyin da zasu bi don maida wannan kudin a lokacin da yakamata. Nasu gudunmawar dai shine su nuna ma wadannan kungiyoyin hanyoyin da zasu bi su samu cin gajiyar wannan bashin. Kuma suna kokari wajen wayar musu da kai da kuma taimaka musu wajen bude asususn ajiya na zamani a bankuna.
A wani ban gare kuma su kan bama mutane shawara wadanda keda sha’awar karbar wannan bashin ta yadda zasu samu registar kungiyarsu da mambobinsu don samun takardun zama gungiya me zaman kanta. Wannan tsarin dai an kirkiroshine don ‘yan Najeriya masu kuzarin dogaro da kai, don haka kowa na iya binciken ina irin wadannan kungiyoyin suke a jihohinsu don su amfana da irin wannan damar.