Kulob din chealsea ya sake daukar wani mataki a gasar kulob kulob na zakarun turai wato English Premier League bayan da dan wasan ta Didier Drogba ya jefa kwallo guda bayan hutun rabin lokaci, John Terry da Ramires ne suka taimaka wa kulob din samun nasarar lashe wasan da ci 3 – 1 a filin wasan Leicester City.
A bangaren Jose Mourinho kuma, kulob din na iya daukar kanbin wasan idan suka doke Crystal Palace a ranar lahadi.
Leicester wadda ta lashe wasannin ta 4 da suka gabata, ita ta fara jefa kwallo ana daf da tafiya hutun rabin lokaci ta kafar dan wasan ta Marc Albrighton sannan kuma ta nuna alamun cewa zata iya cigaba da jan ragamar wasan kafin Chelsea ta sake kara kuzari bayan hutun rabin lokaci.
Chelsea ta kara kaimi bayan minti uku daga dawo wa hutun rabin lokaci ta jefa kwallon ta ta farko .
Branislav Ivanovic ne ya dauko kwallon ta dama daga gefen filin inda ya tura wa drogba yayin dashi kuma ya jefa ta ckin raga abinda ya haddasa murna sosai ganin cewa wannan itace kwallo ta farko da ya ci a wannan shekarar ta 2015.
Drogba ya sake kai farmakin jefa kwallaye har sau biyu amma sai sukai sama.