Cibiyar nazarin jinsin dan Adam ta Jami’ar Bayero dake jihar Kano, wato Centre for Gender studies, ta kaddamar da sabon shirinta na jagoranci da bada shawarwari ga matasa kan harkokin karatu, sanao’i da zamantakewa, a wani mataki na samar da al’uma ta gari.
A karkashin shirin za a mayar da hankali kan matasa maza da mata da basu sami sukunin zuwa makaranta ba da kuma wadanda ke karatu a makarantun sakandire da jami’oi da kuma sauran makarantun ilimi mai zurfi.
Sauran wadanda shirin zai ba fifko sune matasa ‘yan gudun hijira da wadanda ke cikin yanayin tashin hankalin rayuwa daban daban da kuma matasan da suka jajrice wajan samawa kawunansu ayyukan yi domin tallafa masu.
Farfesa A’isha Abdul Isma’il, dake zaman daraktar cibiyar nazarin jinsin dan Adam, ta jami’ar Bayero dake jihar Kano, ta fayyace duk hanyoyin da zasu bi wajan cimma wannan buri.
Kungiyar NSRP dake ayyukan daidaita al’amurra a Najeriya, dake karkashin hukumar raya kasashe ta Birtaniya, na aiki kafada da kafada da cibiyar ta nazarin jinsin dan Adam dake jami;ar Bayero dake jihar Kano.
Domin Karin bayani ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari: