WASHINGTON, DC —
An yankewa wani mutum hukuncin ‘daurin sama da shekaru hudu a gidan Yari, bisa kan laifin fillewa wata Kyanwa kai ba tare da wani dalili ba.
Mutumin mai suna Rudy Espinoza yana zaune ne a garin Salem dake jihar Oregon ta Amurka, jami’an ‘yan sanda sun cafke shi bayan da makwabcin sa ya kira masa jami’an tsaro.
Jami’an sun same shi cikin jini inda suka tambayeshi menene dalilin da yasa ya aikata haka? Rudy ya amsa da cewa saboda muguwar kyanwa ce.
Hakan ne yasa ‘yan sanda suka nemi izinin bincikar gidan Rudy, cikin binciken ne a ‘dakinsa su kayi cikibis da kwayar Ecstasy mai sa maye. Kan hakane alkali ya yankewa matashin hukuncin ‘daurin sama da shekaru hudu a gidan yari.