Wasu masu bincike a Jami’ar Missouri, sun gano cewa yin kishi ko kuma kyashin abokai a dandalin facebook na iya zama sanadin shiga damuwa ga wasu mutane.
An dai yi wannan bincike ne akan wasu ‘dalibai guda dari bakwai, inda aka gano cewar duk mutanen da suke duba ko kuma nazarin abubuwan da suke faruwa a dandalin facebook na zumunci domin ganin yadda rayuwar abokan nasu take, kuma suke gwadawa ta da tasu rayuwa, ko kuma abubuwan da suke faruwa a gare su, ire iren wadannan mutane na iya shiga damuwa.
A ta bakin Margaret Duffy, Farfesa a jami’ar Missouri tace, “sun gano cewa, idan masu ziyarta dandalin facebook suka fara kishin yadda abokanansa rayuwarsu, akwai yiwuwar irin wadannan mutane su fara nuna alamun damuwa,” ta kuma cigaba da cewa “Facebook na iya zama hanya mai amfani ga mutane da dama, amma sai fa idan sunfi amfani da abubuwan suka gani ko ji, domin yin gyara ga yadda suke gudanar da harkokinsu ko rayuwa. Haka kuma na iya zama aibu ga wadansu mutane.
A saboda haka yana muhimmanci masu amfani da shafin facebook suyi la’akari da illarsa domin kaucewa shiga irin wannan hali a lokacinda suka ziyarci shafin facebook.