Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daliban Sakandire Sun Daurawa Junan Su Aure A Jihar Bauchi


Gwamnatin jihar Bauchi ta bada umurnin rufe makarantar sakandire da firamare mai suna Sa'adu Zungur dake jihar. Lamarin ya faru ne biyo bayan gano wasu daga cikin daliban makarantar da daurawa junansu aure ba bisa ka'ida a cikin harabar makarantar.

Dalibin da ya auri abokiyar karatun tasa ya biya kudin sadaki Naira dari biyar, yayin da kuma sauran daliban dake azuzuwan ma'auratan suka tattara kudade domin sayen kayan shagulgula wanda suka gudanar a cikin sirri.

Duk da shike ba aji guda daliban suke ba, amma an jawo hanaklin malaman makarantar akan lamarin makamacin wannan da ya faru a satin da ya gabata da wani dalibi dan aji biyar, SS2, da aka sakaya sunansa ya shirya aure ba bisa ka'ida ba a cikin aji.

Karar kujeri da muryoyin daliban ne ya jawo hankalin malaman da suka rage cikin makarantar bayan kammala daukar darussa, da aka gabatar da aka gabatar a gaban shugaban makarantar Malam Ahmed Zailani, wanda ya gabatar da lamarin a gaban ma'aikatar ilimi ta jihar.

Mujallar Daily Trust, ta wallafa cewa mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Injiniya Nuhu Gidado, da yake jawabi ya bayyana lamarin a matsayin wata babbar annoba dake barazana ga tarbiyya a daukacin al'umma.

Da yake jawabi, mai bada shawara kan harkokin labarai, jiya litini ya bayyana kulle makarantar a ranar juma'a data gabata yayin da aka gano afkuwar lamarin.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG