Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Boko Haram Dara ta ci Gida


Boma-Bomai
Boma-Bomai

Rahotani daga garin Gombe, na bayani cewa wani bom ya tashi a wani unguwar da ake kira kasuwar mata, inda ya janyo sanadiyar rasa rayukan mutane uku, ciki har da dan kunar bakin waken da ya nemi kai harin.

Bom din dai ya tashin ne a cikin keken NAPEP, din da ya dauki wanda ko kuma wadanda suke dauke da bom din.

Wannan tashin bom dai yayi sanadiyar aika mutane ashirin asibiti saboda raunukan da suka ji, Jihar Gombe, dai ta na fuskantar hare-haren bom a cikin ‘yan kwanaki nan.

Wani Bom - 2'45'
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:10 0:00

XS
SM
MD
LG