A lokutta da dama matasa kan raina sana’a ganin cewar wasu sana’o’I kamar kats-kantatun sana’o’I ne da ba kowa yakamata yayisu ba, mafi yawancin matasa basu cika son yin sana’ar yin shayi ba don suna ganin wannan sana’ar tana da wahala ba, amma ba nan gizo ke sakaba.
Malam Abdulhadi Mai Shayi, ya fara wannan sana’ar tashine tun yana almajiri, idan yaje makaranta ya taso sai yaje wajen aikin shi na koyan yadda ake gudanar da sana’ar shayi da kuma yin wanke wanke, wanda daga bisani har yazo ya iya wannan sana’ar, yanzu dai a takaice yana zaman kanshi kuma yana da yara biyu da ke koyon wanna sana’ar a karkashinshi.
Hasalima da wannan sana’ar har Allah yasa yayi aure kuma yasiya fili don ya gina ma kanshi muhallin zama, duk dai da wannan sana’ar har yasamu yaje makarantar boko don yayi dai daito da zamani. Yayi kira ga matasa da su dukufa da neman sana’ar da zasuyi don tallafawa kansu da tattalin arzikin kasa, kada su jira sai anyi musu.