Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Darajar Naira Yasa Jama'a Da Dama Canza Sana'a


zainab Abdullahi
zainab Abdullahi

Karyewar darajar Naira ya tilaswa jama’a da dama canja sana’a masamman masu harkar tafiya kasashen ketare.

Wata matashiya Zainab Abdullahi, wacce itama harkar tafiya kasar Cotonou take yi domin saye da sayarwa tace alamarin ya shafeta wanda hakan ya tilasmata canja sana’a, inda yanzu ta cire sana’ar yin sabulu.

Ta ce rashin samun riba sakamakon hau-hawn farashin canji ya tilasata canja sana’a kuma ta lura cewa wannan sana’arta fiye mata wanda ta ke yi a da, domin a cewarta a gida ake sana’ar kuma ana samun riba dai gwargwado.

Ta kara da cewa wanjan sana’ar da take yi idan ta sa kudin kadan wajan wannan hada sabulun tana samu riba mai yawa kuma ta ce baya ga sabulun wanka da take yi takan hada turarukan mata da sauransu wanda tana cikin gida ake shigowa ana saya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00

XS
SM
MD
LG