Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Donald Trump Ne Ke Gaban Yan Takarar Republican Ta Amurka


Donald Trump ya lashe zabe karo na uku a cikin zabuka hudu da aka gudanar na tsaida dan takara a jihar Nevada ranar Talata da gagarumin rinjaye, inda ya kara tabbatar da kasancewarshi wanda yake kan gaba a cikin wadanda ke nema jam’iyarsu ta Republican ta tsaida su takarar shugaban kasa, kafin babban zaben da za a gudanar na tsaida dan takara a jihohi da dama ranar Talata mai zuwa.

Nasarar ta biyo bayan zama zakara a jihohin New Hampshire da kuma South Carolina, jihohi biyu da babu dan takarar da ya taba lashe zabe a ciki da bai kasance dan takarar jam’iyar Republican ba.

Sai dai har yanzu, Trump yana fuskantar kalubala daga mutane hudu masu neman jam’iyar ta tsaida su takara.

Wani mai sharhi kan lamura Stuart Rothenberg yace, har yanzu Donald Trump yana bukatar nuna cewa, zai iya ci gaba da samun kashi talatin da biyar, ko arba’in ko arba’in da biyar ko kuma hamsin a kai a kai, a zabuka na gaba.

Hamshakin dan kasuwar ya doke abokan takararshi Sanet Ted Cruz na jihar Texas, da Marco Rubio na jihar Florida a zaben fidda dan takarar da aka gudanar a jihar Nevada inda Rubio ya zo na biyu Cruz kuma na uku, sai gwamnan jihar Ohio John Kasich da kuma tsohon likitan fida Ben Carson a baya.

Binciken ra’ayoyin jama’a na baya bayan nanya nuna Trump yana kan gaba a zaben da za a gudanar a jihohi da dama ranar Talata da ake kira Super Tuesday.

Masu neman jam’iyar Democrat ta tsaida su takarar shugaban kasa, zasu fuskanci gwajinsu na karshe ranar asabar a jihar South Carolina kafin babban zaben da za a gudanar ranar Talata. Tsohuwar sakatariyar ma’aikatar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton da saneta daga jihar Vermont Bernie Sanders zasu sake fafatawa bayan zaben tsaida dan takara da aka gudanar a jihar Nevada .

XS
SM
MD
LG