Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

El Kanemi Ta Lallasa Eyimba 2-1


Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya "Super Eagles" a filin wasa na kasa dake Abuja, inda aka lallasa 'yan Ethiopia da ci 4 da babu, lahadi 27 Maris, 2011
Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya "Super Eagles" a filin wasa na kasa dake Abuja, inda aka lallasa 'yan Ethiopia da ci 4 da babu, lahadi 27 Maris, 2011

El Kanemi Warriors ta Maiduguri ta doke Eyimba da ci 2-1 yayin da aka shiga mako na 30 a gasar Premier League ta Najeriya.

An dai buga wasan ne a filin wasa na Karanka da ke Katsina a jiya Lahdi.

Benjamin Turba da Efe Yarhere suka zirawa El Kanemi kwallayenta, wanda haka ya sa Eyimba ta sha kayi a wasannin goma da ta buga a waje.

Masu sharhi dai na cewa wannan babban koma baya ne ga burin club din da ke yunkurin lashe kofin gasar

Saura mintina biyu a tashi kacal Eyimba ta samu ta zira kwallonta guda a ragar El Kanemi.

Yanzu haka El Kanemi na maystai na 13 da maki 39 yayin da Eyimba ke ci gaba da zama a matsayi na daya da maki 55.

Warri Wolves dai ta sha kasha a hanun Abia Warriors da ca ci 2-1 a Umuahia, kana Heartland da Lobi sun tashi canjarsa, wato babu ci ko daya.

Wikki Tourist ta koma matsayi na uku bayan da ta lallasa Bayelsa United da ci 2-0, sannan zakarun gasar Kano Pillars suka tashi kunnen doki da ci 1-1 da Ifeanyi Uba a garin Nnewi.

A lafiya, Nasarawa United ta doke Rangers da ci daya mai ban haushi, yayin da Shooting Stars ta samun nasara akan Akwa United da ci daya da banza.

XS
SM
MD
LG