Facebook ya ce zai fara amfani da fasahar gano fuska don fadawa mutane idan aka yi amfani da hotansu a kafar sada zumuncin, ya kuma tambayesu idan suna son kamfanin ya ajiye samfurin fuskarsu.
A wata sanarwa da kamfanin ya fitar yace zai mayar da wannan fasaha ta zama zabi, don baiwa mutane damar su kare bayanansu, amma kuma wasu mutane zasu so a fada musu idan akayi amfani da hotunansu.
A cewar Facebook wannan fasaha ba zata kasance a kasar Canada da kasashen Turai ba, saboda doka ta haramta amfani da irin wannan fasaha.
Kamfanonin fasaha sun fara amfani da fasahar gano fuska, duk kuwa da tsoron da ake kan yadda za a iya amfani da fasahar ta wata hanya ta daban. A watan Satumba kamfanin Apple ya sanar da cewa masu amfani da sabuwar wayar iPhone X zasu iya yin amfani da fuskarsu wajen bude wayarsu.
Fasahar gano fuska dai ta kasance wani bangare na Facebook tun akalla shekarar 2010, lokacin da kafar sadarwar ta fara baiwa mutane shawarar buga tambari a hotunansu da na wasu.
Facebook Forum