Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fitilar Laser Kan Iya Hargitsa Kwakwalwar Mota Mai Tuka Kanta


laser pointing
laser pointing

Masu bincike kan harkar tsaro sunyi gargadi kan cewar fitila mai hasken laser na iya birkita na’urorin mota mai amfani da kwakwalwa ko kuma mota maras matuki.

A cewar Jonathan Pitit babban masanin kimiyya a wani kamfani da ake kira Security Innovoation yace, wannan fitila mai hasken laser ana iya samun ta kasuwa kan kudin da basu taka kara sun karya ba, kuma ana iya amfani da ita wajen birkita kwakwalwar na’urorin motocin nan maras matuki da aka kashe makurden kudade wajen inganta su wajen saka musu dinbim na’urori masu yawa da suka hada da na’urar ji da ganin duk abinda ke kusa da ita.

Sai dai wannan illa da fitilar ka iya yiwa kwakwalwar na’urar ba lalle bane ta haddasa motar yin hatsari ba, amma na iya hanata aiki ta hanyar rage mata gudu, da tsayawar da bata kamata ba, harma tana iya sakawa a jiye motar.

Kwanan nan ne Petit babban masanin kimiyya ya fara aiki a kamfanin Security Innovation, shi da wani mai suna Steven E. Shladover suka fitar da wata takardar sakamakon bincike da ke nunin shedar yadda wannan fitila ke hargitsa lamarin na’urar, sun dai samo hakan ne ta hanyar gwaje-gwaje da aka gudanar a jami’ar da ake kira ‘University of Cork’s Computer Security Group. Takardar binciken wadda akayi mata suna da yadda za’a iya kai harin kutse ga matoci masu tuka kansu, Petit da Steven ne dai suka yi aiki kan wannan bincike, suka kuma gabatar da sakamakon da suka samo.

XS
SM
MD
LG