Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Flying Eagles Sun Tashi Zuwa Yin Karon Batta a Kasar Senegal


Yan wasan Najeriya ‘yan kasa da shekaru 23, za su kama hanya zuwa Senegal daga Bajul, babban birnin kasar Gambia a yau Laraba, inda suka kwashe kwanaki goma suna atisaye, domin tunkarar gasar ‘yan kasa da shekaru 23 ta nahiyar Afrika.

Wata sanarwa dauke da sa hanun mataimakain darektan yada labarai a hukumar NFF, wato Ademola Olajire, wanda ya ji ta bakin sakataren kungiyar Sirajo Hassan, ta nuna cewa tawagar ‘yan wasan na dauke da mutane 23.

Sanarwar ta kara da cewa za a tafi ne da jami’a 10 da za su raka ‘yan wasan, wadanda za su hau jirgin Arik domin isa Dakar, babban birnin Senegal.

Ana sa ran ‘yan wasan za su buga wasan sada zumunta na karshe, da Baby Scorpions na Gambia da karfe biyar agogon Najeriya.

Har ila yau bayanai na nuni da cewa da za ran sun isa birnin na Dakar za su dangana da Mbour inda a nan kasashen da ke rukunin B za su fafata.

Najeriya za ta fara fafatawa ne da kasar Mali a ranar 29 ga watan Nuwamba, a wani mataki na neman shiga gasar wasannin Olympics da za a yi birnin Rio da ke Brazil.

Sauran kasashen da ke wannan rukuni sun hada da Algeria da Masar baya ga Najeriyar da Mali.

XS
SM
MD
LG