Kungiyar kwallon kafa ta maza ta 'yan kasa da shekaru 20 Flying Eagles zata kara da Burundi a wasan zagaye na biyu na shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka AFCON da za'a buga a shekarar 2017 idan Allah ya kaimu.
Wannan ya biyo bayan cire kungiyoyin kwallon kafa na 'yan kasa da shekaru 17, da kuma kasa da shekaru 20 da hukumar kwallon kafa ta kasar wato Federation Congolaise de Football Association (FECOFA) ta yi daga cikin wadanda zasu buga wasan shiga gasar cin kofin na AFCON 2017.
Sanarwar ta fito a jiya talata 14 ga wannan watan ne a shafin yanar gizo na hukumar kwallon kafa ta kasar FECOFA, inda ta bayyana cewar ta tabbatar da cire kungiyoyin 'yan wasan ta daga wasannin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka na 2017.
Dan haka ne kungiyar kwallon kafa ta 'yan kasa da shekaru 20 ta Zambiya, da 'yan kasa da 20 na Burundi wadanda ya kamata su fuskanci kungiyar 'yan wasan jamhuriyar demokaradiyyar Kongo a zagaye na farko, sun tsallake zuwa zagaye na biyu, kuma zasu hadu da kungiyar Flying Eagles ta Najeriya a watan Mayun wannan shekarar.
Haka kuma a wasnnin 'yan kasa da shekaru 17 na Madagascar 2017, kasar Chadi ta tsallake zuwa zagaye na biyu na shiga gasar biyo bayan fitar da jamhuriyar demokaradiyyar Kongo da aka yi.