A gasar cin kofin kwallon kafa na duniya, na ‘yan kasa da shekaru 20, da za a buga a bazarar bana, a kasar New Zealand, Amurka, ta samu kanta, a rukunin “A” da kasashen Myanmar, Ukraine da mai masaukin baki New Zealand.
Koch din na ‘yan wasan Amurka, Tab Ramos, yace yana da kayatarwa sanin wadanda zasu kasance a rukuninsu.
Ramos, ya fadi cewa zasu gamu da tirjiya daga kasashen New Zealand, Ukraine da Myanmar domin a cewarsa babu kanwar lasa a wasan kwallo.
A wannan karon Amurka, zata fara wasanta ne da kasar Myanmar ranar 30, ga watan Mayu, a Whangarei, sai kuma ranar 2, ga watan Yuni da zata kara da mai masaukin baki New Zealand, sai kuma ranar 5, ga watan inda zasu kara da kasar Ukraine.
Mexico, wace take babbar abokiyar hamayyar Amurka, abokan karawarta sun hada da Uruguay da Serbia.