Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gidauniyar Rochas Zata Ginawa 'Yan Gudun Hijira Makarata a Yola


'Yan gudun Hijira
'Yan gudun Hijira

Gwamnan jahar Adamawa Jibrila Bindow, ya amince da a baiwa gidauniyar Rochas, fili domin gina makaranta ga ‘yan gudun hijira a jahar .

Gwamnan ya bayana haka a yola babban birnin jahar ta Adamawa, ya kuma bukaci masu hannu da shuni dasu sa jari a fanin ilimi domin madogari ne ga ci gaba.

Gwamna ya ce jahar na cikin jahohi da suke koma baya ta fuskar ilimi, ya kuma bada tabbacin taimako ga gidauniyar Rochas, idan bukatar haka ya taso.

Bindow, ya yabawa Gwamna Rochas Okorocha, akan hobbasa sa kan ilimi da kuma yi masa godiya akan gina makarantar Sakandare domin ‘ya’yan talakawa a jahar ta Adamawa.

Yana mai cewa ana yi sadaukar da kome saboda ilimi,domin a cewar sa zaman lafiya ne ke da daraja dade da ilimi.

Rochas Okorocha,wanda shine shugaban gidauniyar ya ce za'a fara ginin makarantar a watan Janairu na shekara mai zuwa yana mai cewa ginin makarantar wani matakin ne ya cika alkawari da gidauniyar tayi cewa zata gina wa masu gidun hijira makaranta.

XS
SM
MD
LG