Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Golden Eaglets Sun Yi Abin Tarihi, Mali Ma Ta Haye


 U 17
U 17

‘Yan wasan Golden Eaglets na Najeriya sun lallasa takwarorinsu na kasar Brazil, wadanda suka shiga filin wasa da kumburin cewar zasu doke zakarun na duniya na samari ‘yan kasa da shekara 17, suka doke su da ci 3-0, yayin da a can gefe kuwa, daya kasar ta Afirka da har yanzu ke cikin wannan gasa ta cin kofin duniya, Mali, ta ci gaba da nuna hazakar tsaron gida ta doke kasar Croatia da ci 1-0 mai ban haushi.

Kasashen biyu na Afirka sun haye zuwa ga wasan kusa da karshe na gasar cin kofin duniyar samari ‘yan kasa da shekara 17 da ake yi a kasar Chile.

Kwallaye ukun da Najeriya ta zura cikin minti 5 kacal, ya kasha guiwar ‘yan wasan Brazil wadanda suka fito da karfi da niyyar lallasa ‘yan Afirkan. Victor Osimhen, wanda ya jefa kwallonsa na 8 a wasanni 5, da Kingsley Michael da kuma Udochukwu Anumudu sune suka jefa wadannan kwallaye uku daya bayan daya cikin mintoci 5. Sauran wasa kuwa, ba ni in b aka aka rika yi har aka tashi.

A bayan wadannan kwallaye uku da Najeriya ta jefa, kyamarar talabijin ta nuno kyaftin na ‘yan Brazil Ronaldo a wurin zaman ‘yan kallo kamar yana kuka. Kyaftin din bai samu buga wasan na jiya ba a saboda an bas hi katin jan kunne a wasan da Brazil ta yi da New Zealand a zagaye na biyu.

Masana tamaula suka ce wannan lamarin, yatyi kam a sosai da abinda ya faru a lokacin gasar cin kofin duniya ta manya ta 2014 da aka yi a Brazil, inda aka nuno kytaftin na Brazil Thiago Silva zaune yana hawaye a lokacin da Jamus ta lallasa Brazil ba tare da kyaftin din nata ba.

Da wannan nasara da Najeriya ta yi a kan Brazil, ta sake yin wani abin tarihin a wannan gasa ta samari ‘yan kasa da shekara 17, inda a yanzu ta shige gaban Brazil ta zamo kasa daya tilo wadda sau 8 ke nan tana kaiwa akalla zuwa wasan kusa da karshe na lashe wannan kofin.

XS
SM
MD
LG